14 Agusta 2026 - 11:07
Source: ABNA24
Isra'ila Da Amerika Sun Tagirgiza Da Saurin Sake Gina Masana'antar Tsaro Ta Iran

Jaridar Jerusalem Post, ta nakalto wasu jami'ai daga sojojin Isra'ila da kuma hukumar leken asiri ta Mossad, ta ruwaito cewa saurin sake gina masana'antar tsaro ta Iran bayan yaƙin da Isra'ila da Amurka suka yi kan Iran, ya ba Isra'ila girgiza da mamaki.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Barnar da aka yi wa masana'antar tsaro ta Iran, a maimakon shekaru da yawa, ta jinkirta ayyukan wannan sashe na 'yan watanni ne kawai. Har ila yau, Iran ta ci gaba da ikon samar da makamai masu linzami na ballistic cikin sauri.

Duk da dubban hare-hare, Iran tana sake gina ƙarfin makamai masu linzami na ballistic da sauri fiye da hasashe, ta yadda za ta iya mayar da ma'ajiyarta zuwa matakin da take kafin yaƙi nan da shekara ta 2027, kuma nan da shekara ta 2028 za ta sake zama "babbar barazana."

...................

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha